Jonatan, ɗan Saul kuwa, yana da ɗa, sunansa Mefiboshet, amma gurgu ne. Yana da shekara biyar sa'ad da aka kawo labarin mutuwar Saul da Jonatan daga Yezreyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi, ta sheƙa a guje. A sa'ad da take gudu sai ya faɗo, sanadin gurguntakar ke nan.
A lokacin nan sai Menahem ya hallaka Tifsa da dukan waɗanda suke cikinta, da karkararta tun daga Tirza, domin ba su karɓe shi ba, saboda haka ya hallaka ta, ya tsattsage dukan matan da suke da juna biyu.
Samariya za ta ɗauki hakkin zunubinta, Gama ta tayar wa Allahnta. Za a kashe mutanenta da takobi. Za a fyaɗa jariranta a ƙasa, A kuma tsage matanta masu ciki.”
Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa, “ ‘Kai ne ka shiryar da 'yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”