Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 24:15 - Littafi Mai Tsarki

15 “Don haka sa'ad da kuka ga mummunan aikin saɓo mai banƙyama, wanda Annabi Daniyel ya faɗa, an tsai da shi a Wuri Mai Tsarki (mai karatu fa yă fahimta),

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 “Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’ wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane),

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 24:15
19 Iomraidhean Croise  

Ni Ubangiji na ce, wannan zai zama muku alama, cewa zan hukunta ku a wannan wuri domin ku sani lalle maganata ta aukar muku da masifa za ta cika.


Sai mutumin nan ya ce mini, “Ɗan mutum ka duba da idonka, ka ji da kunnuwanka, ka kuma mai da hankali ga dukan abin da zan nuna maka, gama saboda haka aka kawo ka nan. Sai ka sanar wa jama'ar Isra'ila abin da ka gani duka.”


A cikin waɗanda aka zaɓa akwai Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya, daga kabilar Yahuza.


Sojojinsa za su ɓata tsattsarkan wuri da kagararsa. Za su kuma hana yin hadayu na yau da kullum, su kafa abin banƙyama da suke lalatarwa.


“Tun daga lokacin da za a hana miƙa hadayar ƙonawa ta yau da kullum, a kafa abin banƙyama, wanda yake lalatarwa, za a yi kwana dubu da ɗari biyu da tasa'in.


A lokacin da ka fara roƙe-roƙenka sai aka ba da umarni, na kuwa zo domin in faɗa maka, gama ana sonka ƙwarai. Sai ka fahimci maganar da wahayin.


Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara.


Wannan shugaba zai yi alkawari mai ƙarfi na shekara bakwai da mutane da yawa. Amma bayan shekara uku da rabi za a hana a yi sadaka da hadaya. Abin ƙyama zai kasance a ƙwanƙolin Haikali, har lokacin da ƙaddara za ta auko wa wanda ya sa abin ƙyama.”


to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.


“Sa'ad da kuka ga an kafa mummunan aikin saɓo mai banƙyama a wurin da bai kamata ba (mai karatu fa yă fahimta), to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.


Don lokaci zai auko muku da maƙiyanku za su yi muku ƙawanya, su yi muku zobe, su kuma tsattsare ku ta kowane gefe,


“Sa'ad da kuka ga rundunonin yaƙi sun kewaye Urushalima, sa'an nan ku tabbata ana kusan ribɗe ta.


In fa muka ƙyale shi kan haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma za su zo su karɓe ƙasarmu su ɗebe jama'armu.”


suna ihu suna cewa, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, ku taimaka! Ga mutumin da yake bi ko'ina yana koya wa mutane su raina jama'armu da Shari'a, da kuma wannan wuri. Banda haka kuma har ma ya kawo al'ummai a cikin Haikalin, ya ƙazantar da wurin nan tsattsarka.”


Sai suka gabatar da masu shaidar zur, suka ce, “Mutumin nan ba ya rabuwa da kushe tsattsarkan wurin nan, da kuma Attaura,


Saboda haka, lalle ne mu ƙara mai da hankali musamman ga abubuwan da muka ji, don kada mu yi sakaci, su sulluɓe mana.


Albarka tā tabbata ga mai karanta maganar nan ta annabci, ta kuma tabbata ga masu ji, waɗanda kuma suke kiyaye abin da yake a rubuce a ciki, domin lokaci ya gabato.


Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan