Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 24:10 - Littafi Mai Tsarki

10 A sa'an nan da yawa za su yi tuntuɓe, su ci amanar juna, su kuma ƙi juna.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 24:10
17 Iomraidhean Croise  

'Dan'uwa zai ba da ɗan'uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. 'Ya'ya kuma za su tayar wa iyayensu, har su sa a kashe su.


Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”


Amma kuwa ba shi da tushe, rashin ƙarƙo gare shi kuma, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru saboda Maganar, sai ya yi tuntuɓe.


Sai suka yi tuntuɓe sabili da shi. Amma Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu da kuma a gidansu.”


Annabawan ƙarya da yawa za su firfito, su ɓad da mutane da yawa.


Ɗan'uwa zai ba da ɗan'uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. 'Ya'ya kuma za su tayar wa iyayensu har su sa a kashe su.


Su kam, ba su da tushe, rashin ƙarƙo gare su, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru domin wannan Magana, nan da nan sai su yi tuntuɓe.


Ko da iyayenku ma da 'yan'uwanku, da danginku, da abokanku, sai sun bāshe ku, su kuma sa a kashe waɗansunku.


Ka dai sani duk waɗanda suke ƙasar Asiya sun juya mini baya, a cikinsu kuwa har da Fijalas da kuma Harmajanas.


domin Dimas, saboda ƙaunar duniyar nan, ya yashe ni, ya tafi Tasalonika. Karaska ya tafi ƙasar Galatiya, Titus kuma ya tafi ƙasar Dalmatiya.


A lokacin da na ba da hanzarina na farko, ba wanda ya goyi bayana, sai duk suka yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan