Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 23:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Kada ku kira kowa ‘Uba’ a duniya, domin Uba ɗaya ne yake gare ku, wanda yake cikin Sama.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Kada kuma ku kira wani a duniya ‘uba,’ gama kuna da Uba ɗaya ne, yana kuwa a sama.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 23:9
16 Iomraidhean Croise  

Da Elisha ya kamu da ciwon ajali, sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi wurinsa, ya yi kuka a gabansa, yana cewa, “Ubana, Ubana, karusar Isra'ila da mahayan dawakanta!”


Elisha kuwa ya gani, ya yi kuka yana cewa, “Ubana, ubana! Mai ikon tsaron Isra'ila! Ka tafi ke nan!” Bai kuwa ƙara ganin Iliya ba. Da baƙin ciki Elisha ya kama tufafinsa ya kece.


Da Sarkin Isra'ila ya gan su, sai ya ce wa Elisha, “Ya mai girma, in karkashe su? In karkashe su?”


Ubangiji Mai Runduna ya ce wa firistoci, “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bara kuwa yakan girmama maigidansa. Ni Ubanku ne, me ya sa ba ku girmama ni ba? Ni kuma Maigidanku ne, me ya sa ba ku ganin darajata? Kun raina ni, duk da haka kuna tambaya cewa, ‘Ƙaƙa muka raina ka?’


Kada kuma a kira ku ‘Shugabanni’, domin Shugaba ɗaya gare ku, wato, Almasihu.


Ai, al'ummai ma suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, Ubanku na Sama kuwa ya san kuna bukatarsu duka.


To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?


“Ya ku 'yan'uwa da shugabanni, ku ji hanzarin da zan kawo muku a yanzu.”


Ko da kuna da malamai masu ɗumbun yawa, amma ba ku da ubanni da yawa, don ni ne ubanku a cikin Almasihu ta wurin bishara.


In kasance Uba a gare ku, Ku kuma ku kasance 'ya'yana, maza da mata, In ji Ubangiji Maɗaukaki.”


Har wa yau kuma, ai, muna da ubanninmu na jiki da suke hore mu, mun kuwa yi musu ladabi. Ashe, ba za mu fi yi wa Uban ruhohinmu biyayya ƙwarai ba, mu rayu?


Ku dubi irin ƙaunar da Uba ya nuna mana, har yake ce da mu 'ya'yan Allah, haka kuwa muke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan