Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 23:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Amma ku kam, kada a ce muku ‘Malam’, domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa 'yan'uwa ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 “Amma kada a kira ku ‘Rabbi,’ gama kuna da Maigida ɗaya ne, ku duka kuwa, ’yan’uwa ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 23:8
34 Iomraidhean Croise  

Ya isa wa almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira maigida Ba'alzabul, to, mutanen gidansa kuma fa?”


Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”


Kada kuma a kira ku ‘Shugabanni’, domin Shugaba ɗaya gare ku, wato, Almasihu.


a gaishe su a kasuwa, a kuma riƙa ce da su ‘Malam’.


Sai Yahuza da ya bashe shi ya ce, “Ko ni ne, ya Shugaba?” Yesu ya ce masa, “Ga shi, kai ma ka faɗa.”


Nan da nan ya matso wurin Yesu, ya ce, “Salama alaikun, ya Shugaba!” Sai ya yi ta sumbantarsa.


Yesu ya ce masa, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce masa, “Malam, in sami gani!”


Bitrus kuwa ya tuna, sai ya ce masa, “Ya Shugaba, dubi! Ɓauren nan da ka la'anta ya bushe!”


Da zuwansa kuwa ya zo wurin Yesu, ya ce masa, “Ya shugaba!” sai ya yi ta sumbantarsa.


Sai Bitrus ya sa baki, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da muke nan wurin, mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.”


Ni kuwa na yi maka addu'a, kada bangaskiyarka ta kāsa. Kai kuma, bayan da ka juyo, sai ka ƙarfafa 'yan'uwanka.”


Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi, wato Malam ke nan, ina kake da zama?”


Sai Nata'ala ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, kai Ɗan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!”


Almajiran suka ce masa, “Ya Shugaba, kwana kwanan nan fa Yahudawa suke neman jifanka, za ka sāke komawa can?”


Yesu ya ce mata, “Maryamu!” Sai ta juya ta ce masa da Yahudanci, “Rabboni!” wato Malam.


Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dad dare, ya ce masa, “Ya Shugaba, mun sani kai malami ne da ka zo daga wurin Allah, domin ba mai iya yin waɗannan mu'ujizan da kake yi, sai ko Allah yana tare da shi.”


Suka kuma zo wurin Yahaya, suka ce masa, “Ya shugaba, wanda dā kuke tare a hayin Kogin Urdun, wanda kai kanka ma ka shaida shi, to, ga shi, yana yin baftisma, har kowa da kowa yana zuwa wurinsa.”


Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Ya shugaba, ci abinci.”


Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Ya Shugaba, yaushe ka zo nan?”


Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Ya Shugaba, wa ya yi zunubi da aka haifi mutumin nan makaho, shi, ko iyayensa?”


Ba cewa muna nuna muku iko a kan bangaskiyarku ba ne, a'a, sai dai muna aiki tare ne, domin ku yi farin ciki, domin a game da bangaskiyarmu kam, kuna tsaye kankan.


Domin ba wa'azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Almasihu a kan shi ne Ubangiji, mu kuwa bayinku ne saboda Yesu.


shi da yake sa wa kowace kabila ta sama da ta ƙasa suna,


ba kuma a kan bawa ba, sai dai a kan abin da ya fi bawa, wato 'dan'uwa abin ƙauna, tun ba ma a gare ni ba, balle fa a gare ka, ta wajen al'amarin jiki da kuma wajen al'amarin Ubangiji.


Ya ku 'yan'uwana, kada yawancinku su zama masu koyarwa, domin kun sani, mu da muke koyarwa za a yi mana shari'a da ƙididdiga mafi tsanani.


Kada ku nuna wa waɗanda suke hannunku iko, sai dai ku zama abin koyi ga garken nan.


Ni ne Yahaya, ɗan'uwanku abokin tarayyarku a cikin tsanani, da mulki, da jimiri da suke a cikin Yesu. Ina a can tsibirin da ake kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu.


Sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada, amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka, waɗanda suke shaidar Yesu. Allah za ka yi wa sujada.” Domin gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon yin annabci.


Amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye maganar littafin nan. Allah za ka yi wa sujada.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan