Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 23:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 “Kome suke yi, suna yi ne don mutane su gani. Sukan yi layunsu fantam-fantam bakin rigunarsu kuma sukan kai har ƙasa;

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 23:5
20 Iomraidhean Croise  

Ya ce, “Ka zo tare da ni, ka ga kishin da nake da shi domin Ubangiji.” Sai suka tafi cikin karusarsa.


Zai zama matuni kamar alama a hannunku, da abin tunawa a goshinku, domin shari'ar Ubangiji ta zama a bakinku, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fisshe ku daga Masar.


Kada ka yarda ka rabu da biyayya da aminci, ka ɗaura su a wuyanka, ka rubuta su kuma a zuciyarka.


A rana ta bakwai kuma firist zai duba cutar, idan mikin bai bazu ba, babu kuma rawayan gashi a cikinsa, zurfin mikin kuwa bai zarce fatar ba,


Ga kuma wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa,


Sai ya ce musu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane. Amma Allah ya san zukatanku. Abin da mutane suke girmamawa ƙwarai, ai, abin ƙyama ne a gun Allah.


Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, masu yin doguwar addu'a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”


Don sun fi ƙaunar girmamawar mutane da girmamawar Allah.


Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karɓar girma a junanku, girman da yake daga Allah Makaɗaici kuwa, ba kwa nemansa?


Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.


“Sai ku riƙe zantuttukan nan nawa a zuciyarku da ranku. Za ku ɗaura su alama a hannuwanku, da goshinku.


“Sai ku yi wa rigar da kukan sa tuntu huɗu, tuntu ɗaya a kowace kusurwa.


Za ku ɗaura su a hannunku da goshinku don alama.


Lalle waɗansu suna wa'azin Almasihu saboda hassada da husuma, amma waɗansu kam, saboda kyakkyawar niyya ne.


Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali'u, kowa yana mai da ɗan'uwansa ya fi shi.


Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gāba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda ake yi wa ibada. Har ma yakan zauna a Haikalin Allah, yana cewa, shi ne Allah.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan