Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 23:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sukan ɗaura kaya masu nauyi, su sa wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu, ba sa ko sa yatsa su taimaka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 23:4
10 Iomraidhean Croise  

“Wannan ne ƙarshen allolin Babila! Dā ana yi wa Bel da Nebo sujada, Amma yanzu ana labtunsu a kan jakuna, Sun zama nawaya a kan dabbobin da suka gaji!


“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na'ana'a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba.


Don haka, sai ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma banda aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa.


Sai Yesu ya ce, “Ku kuma kaitonku, masanan Attaura! Don kuna jibga wa mutane kaya masu wuyar ɗauka, ku da kanku ko ɗan yatsa ba kwa sawa ku tallafa musu!


Saboda haka, don me kuke gwada Allah, ta ɗora wa almajiran nan kayan da mu, duk da kakanninmu, muka kasa ɗauka?


Domin Ruhu Mai Tsarki ya ga ya kyautu, mu ma mun gani, kada a ɗora muku wani nauyi fiye da na waɗannan abubuwa da suke wajibi, wato


Ai, ko waɗanda aka yi wa kaciya ma ba sa kiyaye Shari'a. Sonsu ne a yi muku kaciya, don su yi fāriya da ku a kan an yi muku kaciya.


Domin ƙaunar Allah ita ce mu bi umarninsa, umarninsa kuwa ba matsananta ba ne.


Amma a game da sauranku, ku na Tayatira, da ba sa bin wannan koyarwa, ba su kuma koyi abin da waɗansu suke kira zurfafan al'amuran Shaiɗan ba, ina ce muku, ban ɗora muku wani nauyi ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan