Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 23:37 - Littafi Mai Tsarki

37 “Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

37 “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kike kashe annabawa, kike kuma jifan waɗanda aka aiko gare ki, sau da sau na so in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma kuka ƙi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 23:37
46 Iomraidhean Croise  

“Amma suka yi maka rashin biyayya, suka tayar maka, Suka juya wa dokokinka baya, Suka karkashe anna bawan da suka faɗakar da su, Waɗanda suka faɗa musu su juyo gare ka. Suka yi ta saɓa maka lokaci lokaci.


Ka kiyaye ni kamar yadda ake kiyaye idanu, Ka ɓoye ni a inuwar fikafikanka,


Ina misalin darajar madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji! Mutane sukan sami mafaka a ƙarƙashin fikafikanka.


Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi jinƙai, Gama na zo gare ka neman tsira. Zan sami kāriya a ƙarƙashin fikafikanka, Sai dukan hatsari ya wuce.


Domin kai kake taimakona kullayaumin. Da murna, nake raira waƙa, A inuwar fikafikanka,


Zai rufe ka da fikafikansa, Za ka zauna lafiya a ƙarƙashinsu. Amincinsa zai tsare ka, ya kiyaye ka.


Akwai abin da ban yi mata ba? Me ya sa ta yi 'ya'yan inabi masu tsami, maimakon 'ya'yan inabi masu kyau da nake sa zuciya.


“Don me mutanena ba su amsa ba Sa'ad da na je wurinsu domin in cece su? Don me ba su amsa ba sa'ad da na yi kiransu? Ba ni da isasshen ƙarfin da zan fanshe su ne? Ina da iko in sa teku ya ƙafe ta wurin umarnina, Ina kuma da iko in sa rafuffukan ruwa su zama hamada, Kifayen da suke ciki su mutu saboda rashin ruwa.


Na hori 'ya'yanku, amma a banza, ba su horu ba, Kun kashe annabawanku da takobi kamar mayunwacin zaki.


Suka kamo Uriya daga Masar suka kawo shi wurin sarki Yehoyakim, sai ya sa aka kashe shi da takobi, aka binne gawarsa a makabartar talakawa.


Wannan birni ya tsokane ni ƙwarai tun lokacin da aka gina shi har zuwa yau, domin haka zan kawar da shi daga gabana.


Na yi ta aiko muku da bayina annabawa, ina cewa, kowa ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara ayyukansa, kada ya bauta wa gumaka. Ta haka za ku zauna a ƙasa wadda na ba ku, ku da kakanninku, amma ba ku kasa kunne, ku ji ni ba.


Sarki ya umarci Yerameyel ɗan sarki, da Seraiya ɗan Azriyel da Shelemiya ɗan Abdeyel, su kamo Baruk magatakarda da annabi Irmiya, amma Ubangiji ya ɓoye su!


Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki, Domin a cece ki, Har yaushe mugayen tunaninki za su yi ta zama a cikinki?


Na yi ta aika muku da dukan bayina annabawa waɗanda suka faɗa muku kada ku aikata wannan mugun abin banƙyama.


Ku ji faɗaka, ya ku mutanen Urushalima, Don kada a raba ni da ku, Don kada in maishe ku kufai, Ƙasar da ba mazauna ciki.”


Yawan kiransu, yawan tayarwar da suke yi mini, Sai ƙara miƙa wa Ba'al sadaka suke yi, Suna ƙona turare ga gumaka.


Mutanena sun himmantu su rabu da ni, Ko da yake an kira su ga Ubangiji, Ba wanda ya girmama shi.


“Tasu ta ƙare, gama sun ratse, sun rabu da ni. Halaka za ta auka musu domin sun tayar mini. Ko da yake zan cece su, duk da haka suna faɗar karya a kaina.


Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka yi ta yi musu shela suna cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, ku bar mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku.’ Amma ba su ji ba, ba su kuwa kula ba, ni Ubangiji na faɗa.


Sai ya aiki bayinsa su kirawo waɗanda aka gayyata bikin, amma waɗanda aka gayyatar suka ƙi zuwa.


Sauran kuwa suka kame bayinsa, suka wulaƙanta su, suka kashe su.


Kuna cewa, ‘Da mun zauna a zamanin kakanninmu, da ba mu taya su zub da jinin annabawa ba.’


Ta haka kuka shaidi kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa.


Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a Sama, gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku.”


Amma wan ya yi fushi, ya ƙi shiga. Ubansa kuwa ya fito, ya yi ta rarrashinsa.


waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa, suka kuma kore mu, ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuma da dukan mutane,


Sai na ga matar ta bugu da jinin tsarkaka, da kuma jinin mashaidan Yesu. Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai da gaske.


Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda kika zo neman mafaka gare shi, ya sāka miki da cikakken lada saboda abin da kika yi.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan