Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 23:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami'unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 Saboda haka ina aika muku da annabawa, da masu hikima da malamai. Waɗansunsu za ku kashe ku kuma gicciye; waɗansu kuma za ku yi musu bulala a majami’unku kuna kuma binsu gari-gari.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 23:34
36 Iomraidhean Croise  

Ubangiji kuwa ya yi magana ta wurin bayinsa annabawa ya ce,


Amma suka yi masa maƙarƙashiya, sarki kuma ya ba da umarni, suka jejjefi annabin da duwatsu har ya mutu a farfajiyar Haikalin Ubangiji.


Adalci yana rayar da mutum, wanda yake da hikima kuma yakan ceci rayuka.


Sa'ad da Irmiya ya gama faɗar dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa wa dukan jama'a, sai firistoci, da annabawa, da dukan jama'a suka kama shi, suna cewa, “Mutuwa za ka yi!


Sarki ya umarci Yerameyel ɗan sarki, da Seraiya ɗan Azriyel da Shelemiya ɗan Abdeyel, su kamo Baruk magatakarda da annabi Irmiya, amma Ubangiji ya ɓoye su!


In sun tsananta muku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Gaskiya, ina gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Ɗan Mutum zai zo.


Sai ya ce musu, “To, duk malamin Attaura da ya zama almajirin Mulkin Sama, kamar maigida yake, wanda ya ɗebo dukiya sabuwa da tsohuwa daga taskarsa.”


Ta haka kuka shaidi kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa.


a kuma yi wa dukan al'ummai wa'azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima.


Za su fisshe ku daga jama'a. Hakika, lokaci ma na zuwa da kowa ya kashe ku, zai zaci bautar Allah yake yi.


Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama alaikun! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma na aike ku.”


Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”


To, a kwanakin nan waɗansu annabawa suka zo Antakiya daga Urushalima.


har ma ya sare Yakubu ɗan'uwan Yahaya da takobi.


To, a Ikkilisiyar da take Antakiya akwai waɗansu annabawa, da masu koyarwa, wato Barnaba, da Saminu wanda ake kira Baƙi, da Lukiyas Bakurane, da Manayan wanda aka goya tare da sarki Hirudus, da kuma Shawulu.


Amma waɗansu Yahudawa suka zo daga Antakiya da Ikoniya, da suka rarrashi taron, suka jejjefe Bulus suka ja shi bayan gari, suna zato ya mutu.


Yahuza da Sila kuma, da yake su annabawa ne, suka gargaɗi 'yan'uwa da maganganu masu yawa, suka kuma ƙarfafa su.


Sai suka bi shawara tasa, suka kuma kirawo manzannin, suka yi musu dūka, suka kwaɓe su kada su ƙara magana da sunan Yesu, sa'an nan suka sake su.


Duk da haka dai muna sanar da hikima ga waɗanda suka kammala, sai dai ba hikimar wannan zamani ba, ba kuwa ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda suke shuɗewa ba.


Kamar gwanin magini, haka na sa harsashin gini, gwargwadon baiwar alherin da Allah ya yi mini, wani kuma yana ɗora gini a kai. Sai dai kowane mutum, yă lura da irin ginin da yake ɗorawa a kai.


Shi ne kuwa muke sanarwa, muna yi wa kowane mutum gargaɗi, muna kuma koya wa kowane mutum da matuƙar hikima, da nufin mu miƙa kowane mutum cikakke a cikin Almasihu.


suna hana mu yi wa al'ummai wa'azi, don kada su sami ceto. Ta haka a kullum suke cika mudun zunubansu. Amma fa fushin Allah ya aukar musu.


Aka jejeffe su da duwatsu, an gwada su, aka raba su biyu da zarto, aka sare su da takobi. Sun yi yawo saye da buzun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, da ƙunci, da wulakanci.


Mazaunan duniya kuma, sai su yi ta alwashi a kansu, suna ta shagali, suna a'aika wa juna da kyauta, domin annabawan nan biyu dā sun azabtar da mazaunan duniya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan