A wannan rana mutanen da suke zaune a gaɓar Filistiyawa za su ce, ‘Dubi abin da ya faru ga jama'ar da muka dogara da su don su tsare mu daga Sarkin Assuriya! Ƙaƙa za mu yi mu tsira?’ ”
Amma da Yahaya ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa, sun taho domin a yi musu baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa?
Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.
Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.
Amma ina tsoro kada yă zamana, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa'u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Almasihu.
To mutumin da ya raina Ɗan Allah, ya kuma tozarta jinin nan na tabbatar alkawari, wanda aka tsarkake shi da shi, har ya wulakanta Ruhun alheri, wane irin hukunci mafi tsanani kuke tsammani ya cancanta fiye da wancan?
Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama?
to, ta ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji kansa, shi ne ya fara sanar da shi, waɗanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi,
Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi.