Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami'unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba.
“Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi!
Sai ya ce masa ‘Kai mugun bawa! Zan yi maka shari'a bisa ga abin da ka faɗa da bakinka. Ashe, ka sani ni mutum ne mai tsanani, mai son banza, ina kuma girbar abin da ba ni na shuka ba?