Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 23:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Kai makaho Bafarisiye! Ka fara wanke cikin kwaf da kwano, sa’an nan bayan ma zai zama da tsabta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 23:26
12 Iomraidhean Croise  

Bari mugaye su bar irin al'amuransu, Su sāke irin tunaninsu. Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu, Shi mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.


Na ga abubuwanku masu banƙyama, Wato zinace-zinacenku, da haniniya kamar dawakai, Da muguwar sha'awarku ta karuwanci a kan tuddai da filaye, Ya Urushalima, taki ta ƙare! Har yaushe za a tsarkake ki?”


Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki, Domin a cece ki, Har yaushe mugayen tunaninki za su yi ta zama a cikinki?


Ku rabu da laifofin da kuka yi mini, sa'an nan ku samo wa kanku sabuwar zuciya da sabon hali. Don me za ku mutu, ya ku jama'ar Isra'ila?


“Ko dai ku ce itace kyakkyawa ne, 'ya'yansa kuma kyawawa, ko kuwa ku ce itace mummuna ne, 'ya'yansa kuma munana. Don itace, da 'ya'yansa ake gane shi.


Amma da uwa tasa ta zuga ta, sai ta ce, “A ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi yanzu yanzu.”


In sun komo daga kasuwa kuwa, ba sa cin abinci sai sun yi wanka tukuna. Akwai kuma waɗansu al'adu da yawa da suka gada suke kiyayewa, kamar su wankin ƙore, da tuluna, da daruna.


Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ku Farisiyawa kam, kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike kuke da zalunci da mugunta.


Mutumin kirki kam ta kyakkyawar taskar zuciyarsa yakan yi abin kirki, mugu kuwa ta mummunar taskar zuciyarsa yakan yi mugun abu. Ai, abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.”


Ya ku ƙaunatattu, tun da aka yi mana waɗannan alkawarai, sai mu tsarkake kanmu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, da bangirma ga Allah mu kamalta a cikin tsarki.


sai mu matsa kusa, da zuciya ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatunmu tsarkakakku daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa.


Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al'amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan