“Kai kuma, Ezra, bisa ga hikimar da Allahnka ya ba ka, sai ka naɗa mahukunta da alƙalai waɗanda za su yi wa mutanen da suke a lardin Yammacin Kogi shari'a, wato dukan waɗanda suka san shari'a. Waɗanda ba su san shari'a ba kuwa, sai ka koya musu.
Ezra ɗin ya taho daga Babila. Shi malami ne, masanin shari'ar Musa, wadda Ubangiji Allah na Isra'ila ya bayar. Sarki kuwa ya ba shi dukan abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.
Gama ya kamata bakin firist ya kiyaye ilimi, wajibi ne firistoci su koyar da ilimin gaskiya na Allah, a gare su mutane za su tafi su koyi nufina, domin su manzannina ne, ni Ubangiji Mai Runduna.
“Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo a cikin manyan riguna, masu so a gaishe su a kasuwa, masu son mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki.