Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 23:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Kukan ce, ‘Kowa ya rantse da bagaden hadaya, ba kome. Amma duk wanda ya rantse da sadakar da aka ɗora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Kukan kuma ce, ‘In wani ya rantse da bagade, ba damuwa; amma in ya rantse da bayarwar da take bisansa, sai rantsuwar ta kama shi.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 23:18
7 Iomraidhean Croise  

“Idan wani ya yi wa maƙwabcinsa laifi, har aka sa shi ya rantse, ya kuwa zo ya rantse a gaban bagaden a wannan Haikali,


Idan mutum ya yi wa'adi ga Ubangiji, ko kuwa ya rantse zai yi wani abu, ko kuwa ba zai yi wani abu ba, to, kada ya warware maganarsa, amma sai ya aikata abin da bakinsa ya hurta.


“Kaitonku, makafin jagora, ku da kuke cewa, ‘Kowa ya rantse da Haikalin ba kome, amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, sai rantsuwarsa ta kama shi.’


Ku makafi, wawaye! Wanne ya fi girma, zinariyar ce ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar?


Ku makafi! Wanne ya fi girma, sadakar ko kuwa bagaden hadaya da yake tsarkake sadakar?


Amma ku kukan ce, ‘In mutum ya ce wa ubansa ko uwa tasa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni ya zama Korban,” ’ (wato an sadaukar),


Ina sāke tabbatar wa duk wanda ya yarda a yi masa kaciya, cewa wajibi ne ya bi dukkan Shari'a.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan