Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 23:16 - Littafi Mai Tsarki

16 “Kaitonku, makafin jagora, ku da kuke cewa, ‘Kowa ya rantse da Haikalin ba kome, amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, sai rantsuwarsa ta kama shi.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 “Kaitonku, makafi jagora! Kukan ce, ‘In wani ya rantse da haikali, ba damuwa; amma in ya rantse da zinariyar haikali, sai rantsuwar ta kama shi.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 23:16
14 Iomraidhean Croise  

Su waɗanda suke bi da jama'an nan, sun bashe su, sun ruɗar da su ɗungum.


Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai, duk biyu sai su faɗa a rami.”


“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga.


Ku makafi, wawaye! Wanne ya fi girma, zinariyar ce ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar?


Ku makafi! Wanne ya fi girma, sadakar ko kuwa bagaden hadaya da yake tsarkake sadakar?


Makafin jagora, kukan tace ƙwaro ɗan mitsil, amma kukan haɗiye raƙumi!


Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.


Ina sāke tabbatar wa duk wanda ya yarda a yi masa kaciya, cewa wajibi ne ya bi dukkan Shari'a.


Amma fiye da kome, 'yan'uwana, kada ku rantse sam, ko da sama, ko da ƙasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. Sai dai in kun ce “I”, ya tsaya a kan “I” ɗin kawai, in kuwa kun ce “A'a”, ya tsaya a kan “A'a” ɗin kawai, don kada a hukunta ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan