14 [Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan ci kayan matan da mazansu sun mutu, kukan yi doguwar addu'a don ɓad da sawu. Saboda haka za a yi muku hukunci mafi tsanani.]
“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga.
Wanda kuwa bai san nufin ubangijinsa ba, ya kuma yi abin da ya isa dūka, za a doke shi kaɗan. Duk wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.”
A cikinsu kuwa akwai masu saɗaɗawa su shiga gidajen mutane, suna rinjayar mata marasa wayo, waɗanda zunubi ya sha kansu, muguwar sha'awa iri iri kuma ta ɗauke musu hankali,