Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 23:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi, duk kuma wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 23:12
15 Iomraidhean Croise  

Allah yakan ƙasƙantar da mai girmankai, Yakan ceci mai tawali'u.


Ko da yake Ubangiji yana can Sama, Duk da haka yana kulawa da masu kaɗaici. Masu girmankai kuwa ba za su iya ɓoye kansu daga gare shi ba.


Tsoron Ubangiji koyarwa ce domin samun hikima. Sai ka zama mai tawali'u kafin ka sami girmamawa.


Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.


Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.


Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin Samaniya, ina ɗaukaka shi, ina kuma girmama shi saboda dukan ayyukansa daidai ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Yakan ƙasƙantar da masu girmankai.”


Duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar ɗan yaron nan, ai, shi ne mafi girma a Mulkin Sama.


“Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin Sama nasu ne.


Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”


Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”


Allah shi yake yin mayalwacin alheri. Domin haka Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali'u alheri.”


Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”


Don haka, sai dai ku ƙasƙantar da kanku ga maɗaukakin ikon Allah, domin ya ɗaukakaku a kan kari.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan