Gama Sarkin Babila yana tsaye a mararrabar hanya, inda hanyar ta rabu biyu, yana yin dūbā, yana girgiza kibau, yana neman shawara wurin kan gida, yana dūbān hanta.
Ba daidai ba ne ka tsaya a mararraba, Don ka kashe waɗanda suke ƙoƙarin tserewa. Ba daidai ba ne ka ba da waɗanda suka tsere a hannun maƙiyansu A ranar wahala.”