6 Sauran kuwa suka kame bayinsa, suka wulaƙanta su, suka kashe su.
6 Sauran suka kama bayinsa suka wulaƙanta su, suka kuma kashe su.
Amma suka ƙi kula, suka tafi abinsu, wani ya tafi gona tasa, wani kuma cinikinsa.
Sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus.
Gama za a bāshe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa yau.
Shawulu kuwa yana goyon bayan kisan Istifanas. A ran nan kuwa wani babban tsanani ya auko wa Ikkilisiyar da take Urushalima. Duk aka warwatsa su a lardin Yahudiya da na Samariya, sai dai manzannin kawai.
Ku riƙa tunawa da waɗanda suke kurkuku, kamar tare kuke a ɗaure, da kuma waɗanda ake gwada wa wuya, kamar ku ake yi wa.