Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 22:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Amma suka ƙi kula, suka tafi abinsu, wani ya tafi gona tasa, wani kuma cinikinsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 “Amma ba su kula ba, suka kama gabansu, ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya kuma ya tafi kasuwancinsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 22:5
21 Iomraidhean Croise  

Sai Lutu ya fita ya faɗa wa surukansa waɗanda za su auri 'ya'yansa mata, “Tashi, ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma sai surukansa suka aza wasa yake yi.


Sa'an nan Yakubu ya ba Isuwa gurasa da faten wake, ya ci ya sha, ya tashi ya yi tafiyarsa. Ta haka Isuwa ya banzatar da matsayinsa na ɗan fari.


In kana so ilimi dole ne ka fara da tsoron Ubangiji. Jahilai ba su san darajar hikima ba, sun kuwa ƙi su koya.


Wanda ya faɗa cikin ƙaya kuwa, shi ne wanda ya ji Maganar, amma taraddadin duniya da jarabar dukiya sukan sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.


Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, “Ga shi, na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya kome, ku zo bikin mana!” ’


Sauran kuwa suka kame bayinsa, suka wulaƙanta su, suka kashe su.


Ya ce da dillalan tattabarai, “Ku kwashe waɗannan daga nan, kada ku mai da Haikalin Ubana kasuwa.”


Amma waɗansu suka yi ba'a suka ce, “Ruwan inabi suka sha suka yi tatul!”


Bulus yana ba da bayani a kan adalci, da kamunkai, da kuma hukuncin nan mai zuwa, Filikus ya kaɗu, ya kāda baki ya ce, “Yanzu kam, sai ka koma. In na sami zarafi nā kira ka.”


Ko kuwa kana raina yalwar alherinsa, da jimirinsa, da kuma haƙurinsa ne? Ashe, ba ka sani ba alherin Allah yana jawo ka zuwa ga tuba?


Ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga ala'muran Ruhu kuwa rai ne da salama.


da maciya amana, da masu taurinkai, da masu homa, da masu son annashuwa fiye da son Allah,


to, ta ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji kansa, shi ne ya fara sanar da shi, waɗanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi,


Mahaɗantan malaman nan na ƙarya za su ribace ku da tsararrun labarunsu. An riga an yanke hukuncinsu tun dā, wanda zai hallaka su a shirye yake sosai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan