Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 22:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, “Ga shi, na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya kome, ku zo bikin mana!” ’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 “Sai ya sāke aiken waɗansu bayi ya ce, ‘Ku ce wa waɗanda aka gayyata cewa na shirya abinci. An yanka bijimai da shanun da aka yi kiwo, kome a shirye yake. Ku zo bikin auren mana.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 22:4
18 Iomraidhean Croise  

Suka ƙi yin biyayya, Suka manta da dukan abin da ka yi, Suka manta da al'ajaban da ka aikata. Cikin fāriyarsu suka zaɓi shugaba, Don su koma cikin bauta a Masar. Amma kai Allah ne mai gafartawa, Kai mai alheri ne, mai ƙauna, Jinƙanka da girma yake, ba ka yashe su ba.


Ya Ubangiji, kai managarci ne, mai yin gafara, Cike kake da madawwamiyar ƙauna ga dukan waɗanda suke yin addu'a gare ka.


Gara cin mabunƙusa tare da waɗanda kake ƙauna, da ka ci abinci mai romo a inda ƙiyayya take.


Na shiga cikin lambuna, budurwata, amaryata, Ina tattara mur da ƙaro. Ina shan zuma da kakinsa. Ina shan ruwan inabi da madara kuma. Ƙaunatattuna, ku ci ku sha, har ku bugu da ƙauna!


Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka.


Amma suka ƙi kula, suka tafi abinsu, wani ya tafi gona tasa, wani kuma cinikinsa.


Sa'an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin fa ya shiryu sosai, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba.


Da lokacin biki ya yi, sai ya aiki bawansa yă ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, duk an shirya kome,’


Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”


Sai Bulus da Barnaba suka yi magana gabagaɗi, suka ce, “Ku, ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da yake kun ture ta, kun nuna ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, za mu juya ga al'ummai.


Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai ba mu kome tare da shi hannu sake ba?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan