Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 22:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sai ya aiki bayinsa su kirawo waɗanda aka gayyata bikin, amma waɗanda aka gayyatar suka ƙi zuwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Sai ya aiki bayinsa su kira waɗanda aka gayyata zuwa bikin, amma waɗanda aka ce su zo bikin, suka ƙi zuwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 22:3
30 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya ba da umarni, Sai mata masu yawa suka baza labari cewa,


Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya ce wa jama'a, “Ku komo gare ni a natse, ku dogara gare ni. Sa'an nan za ku zama ƙarfafa ku zauna lafiya.” Amma ba ku yarda ba!


Ba ku saurara ba, ba ku kasa kunne don ku ji ba, ko da yake Ubangiji ya yi ta aiko muku da dukan bayinsa annabawa,


Na yi ta aiko muku da bayina annabawa, ina cewa, kowa ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara ayyukansa, kada ya bauta wa gumaka. Ta haka za ku zauna a ƙasa wadda na ba ku, ku da kakanninku, amma ba ku kasa kunne, ku ji ni ba.


Yawan kiransu, yawan tayarwar da suke yi mini, Sai ƙara miƙa wa Ba'al sadaka suke yi, Suna ƙona turare ga gumaka.


Mutanena sun himmantu su rabu da ni, Ko da yake an kira su ga Ubangiji, Ba wanda ya girmama shi.


Ku yi tsit a gaban Ubangiji Allah! Gama ranar Ubangiji ta gabato. Ubangiji ya shirya ranar shari'a, Ya kuma keɓe waɗanda za su aikata hukuncinsa.


Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar.


“Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi!


yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.”


Sai Yesu ya ce musu, “Abokan ango sa yi baƙin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.


“Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko gare ku! Sau nawa ne ina so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta a cikin fikafikanta, amma kun ƙi!


Amma wan ya yi fushi, ya ƙi shiga. Ubansa kuwa ya fito, ya yi ta rarrashinsa.


Waɗannan maƙiya nawa kuwa, da ba sa so in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.’ ”


Duk da haka, kun ƙi zuwa wurina ku sami rai.


Amma da Yahudawa suka ga taro masu yawa, suka yi kishi gaya, suka yi ta musun abubuwan da Bulus ya faɗa, suna zaginsa.


Amma a game da isra'ila, sai ya ce, “Yini zubur ina miƙa hannuwana ga jama'a marasa biyayya, masu tsayayya.”


Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama?


Saboda haka, shi ne matsakancin sabon alkawari, domin waɗanda aka kira su karɓi dawwamammen gādon da aka yi musu alkawari, tun da yake an yi wata mutuwa mai fansar waɗanda suke keta umarni a game da alkawarin farko.


Ruhu da amarya suna cewa, “Zo.” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta.


Da shigarku garin, za ku same shi kafin ya tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu, gama jama'a ba za su ci ba, sai ya je ya sa albarka a sadakar, sa'an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura yanzu, za ku same shi nan da nan.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan