Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 22:24 - Littafi Mai Tsarki

24 suka ce, “Malam, Musa dai ya ce, ‘In mutum ya mutu, bai bar na baya ba, sai lalle ɗan'uwansa ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Suka ce “Malam, Musa ya faɗa mana cewa in mutum ya mutu ba shi da ’ya’ya, dole ɗan’uwansa yă auri gwauruwar yă kuma haifar wa ɗan’uwan ’ya’ya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 22:24
14 Iomraidhean Croise  

Yahuza kuwa ya ce wa Tamar surukarsa, “Yi zaman gwauranci a gidan mahaifinki, har ɗana Shela ya yi girma,” gama yana jin tsoro kada shi kuma ya mutu kamar 'yan'uwansa. Saboda haka Tamar ta tafi ta zauna a gidan mahaifinta.


Sa'an nan Yahuza ya ce wa, Onan, “Shiga wurin matar ɗan'uwanka, ka yi mata wajibin ɗan'uwan miji, ka samar wa ɗan'uwanka zuriya.”


Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai.


To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza bakwai a cikinmu. Na farkon ya yi aure, da ya rasu, da yake bai haifu kuma ba, sai ya bar wa ɗan'uwansa matarsa.


“Malam, wane umarni ne mafi girma a cikin Attaura?”


“Ba duk mai ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji,’ ne zai shiga Mulkin Sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so.


“Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar mata tasa ba ɗa, sai lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.


suka tambaye shi suka ce, “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba ɗa, lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.


To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”


“Don me kuke kirana, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ba kwa kuwa yin abin da na faɗa muku?


Amma Na'omi ta ce musu, “Ku koma, 'ya'yana, don me za ku tafi tare da ni? Ina da sauran 'ya'ya maza a cikina ne da za su zama mazajenku?


Ki dakata nan sai gobe, da safe za mu gani, idan shi zai cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Idan ya cika, to, da kyau, amma idan bai cika ba, na rantse da Allah mai rai, zan cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Ki kwanta sai da safe.”


Sa'an nan Bo'aza ya ce, “A ranar da ka sayi gonar daga hannun Na'omi, sai kuma ka ɗauki Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayin, domin ka ta da zuriyar da za ta gaji marigayin.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan