Ya ce, “I, yakan bayar.” Da ya dawo gida kuma, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce, “Me ka gani, Bitrus? Wurin wa sarakunan duniya suke karɓar kuɗin fito ko haraji, a wurin 'ya'yansu, ko kuwa daga wurin waɗansu?”
Amma wannan bawa, da fitarsa sai ya tarar da wani abokin bautarsa, wanda yake bi dinari ɗari bashi. Ya cafi wuyarsa, ya ce, ‘Biya ni abin da nake binka.’
Sai na ji kamar wata murya a tsakiyar rayayyun halittar nan huɗu tana cewa, “Mudun alkama dinari guda, mudu uku na sha'ir dinari guda, sai dai kada ka ɓāta mai da kuma ruwan inabi!”