Sarki ya sani fa, idan an sāke gina birnin, aka kuma gama garun, ba za su biya haraji ko kuɗin shiga da fita na kaya ko kuɗin fito ba, baitulmalin sarki za ta rasa kuɗi ke nan.
Muna kuma sanar da ku, cewa ba daidai ba ne ku karɓi haraji, da kuɗin shiga da fita, daga wurin firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da matsaran ƙofa, da masu lura da Haikali, da ma'aikatan wannan Haikali na Allah.
Amfanin ƙasa duk yana tafiya ga sarakunan Da ka ɗora su a kanmu saboda mun yi zunubi. Suna yi mana yadda suka ga dama, mu da dabbobinmu, Muna cikin baƙin ciki.”
cewa in kun ratse, to, a bakin ranku. Gama kun aike ni wurin Ubangiji Allah cewa, ‘Ka roƙar mana Ubangiji Allahnmu. Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya ce ka faɗa mana kuma za mu aikata.’
Ya ce, “I, yakan bayar.” Da ya dawo gida kuma, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce, “Me ka gani, Bitrus? Wurin wa sarakunan duniya suke karɓar kuɗin fito ko haraji, a wurin 'ya'yansu, ko kuwa daga wurin waɗansu?”
A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tibariyas, Buntus Bilatus yana mulkin Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, ɗan'uwansa Filibus yana sarauta Ituriya da Tarakunitas, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiliya,
Bayansa kuma, a lokacin ƙirgen mutane, wai shi Yahuza Bagalile ya ɓullo, ya zuga waɗansu suka yi turu, suka bi shi. Shi ma ya hallaka, duk mabiyansa ma aka warwatsa su.