Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 22:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Sai ya ce masa, ‘Malam, ta yaya ka shigo nan ba tare da sa riga irin ta biki ba?’ Mutumin kuwa ya rasa ta cewa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 22:12
13 Iomraidhean Croise  

Yakan sa matalauta su sa zuciya, Ya sa mugaye su yi shiru.


Da adalai suka ga wannan, sai suka yi murna, Mugaye kuwa aka rufe bakinsu.


Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar da kanka ba, Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba'al ba? Ka duba hanyarka ta zuwa cikin kwari, ka san abin da ka yi. Kana kama da taguwa, mai yawon neman barbara.


“Kamar yadda ɓarawo yakan sha kunya sa'ad da aka kama shi, Haka nan mutanen Isra'ila za su sha kunya, Da su, da sarakunansu, da shugabanninsu, Da firistocinsu, da annabawansu.


Sai ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Abokina, ai, ban cuce ka ba. Ashe, ba mu yi lada da kai a kan dinari guda ba?


Yesu ya ce masa, “Abokina, abin da ya kawo ka ke nan?” Suka matso suka ɗanke Yesu, suka kama shi.


Ina dai gaya muku, in adalcinku bai fi na malaman Attaura da Farisiyawa ba, ba za ku shiga Mulkin Sama ba faufau.”


To, mun sani duk abin da Shari'a ta ce, ya shafi waɗanda suke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma tă sani ƙarƙashin hukuncin Allah take.


Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.


Ka dai sani irinsa ɓatacce ne, mai yin zunubi, shi kansa ma ya sani haka yake.


“Zai kiyaye rayukan amintattun mutanensa, Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu, Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan