Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Hosanna a cikin sama!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:9
11 Iomraidhean Croise  

Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ku yabi Ubangiji daga sama, Ku da kuke zaune a tuddan sama.


Da ya shiga Urushalima dukkan birnin ya ruɗe, ana ta cewa, “Wane ne wannan?”


Amma manyan firistoci da malaman Attaura suka ga abubuwan al'ajabi da ya yi, har yara suna sowa a Haikalin suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji haushi.


Ina dai gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”


Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna ɗaga murya suna cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu.”


Ga shi, an bar muku gidanku a yashe! ina kuwa gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”


“Ɗaukaka ga Allah ta tabbata, can cikin Sama mafi ɗaukaka. A duniya salama ta tabbata, ga mutanen da yake murna da su matuƙa.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan