Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:5 - Littafi Mai Tsarki

5 “Ku ce wa 'yar Sihiyona, Ga Sarkinki yana zuwa gare ki, Mai tawali'u ne, Yana kan aholaki, wato, ɗan jaki.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 “Ku ce wa Diyar Sihiyona, ‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki, mai tawali’u yana a kan jaki, a kan aholaki, ɗan jaki.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:5
39 Iomraidhean Croise  

Yana riƙe da sandan mulkinsa, Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa, Har Shilo ya zo. Zai mallaki dukan jama'o'i.


Sarki kuwa ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo abubuwan nan?” Ziba ya amsa, ya ce, “An kawo wa iyalin sarki jakuna su hau, da abinci, da 'ya'yan itace, domin samari su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suke rafkewa a jejin su sha.”


ya ce musu, “Ku tafi tare da fādawana, ku sa Sulemanu, ɗana, ya hau alfadarina, ku kai shi Gihon,


Sulemanu kuwa ya tattara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), waɗanda ya zaunar da su a biranen karusai da kuma waɗansu tare da shi a Urushalima.


Domin in iya tsayawa a gaban jama'ar Urushalima, In faɗa musu dukan abin da ya sa nake yabonka. Zan yi farin ciki saboda ka cece ni.


Bari dukan waɗanda suke zaune a Sihiyona su yi sowa su raira waƙa! Gama Mai Tsarki, Allah na Isra'ila, mai girma ne, Yana zaune tare da mutanensa.”


Ki haura a kan dutse mai tsayi, ke Urushalima, Ki faɗi albishir! Ki yi kira da babbar murya, ya Sihiyona, Ki faɗi albishir! Yi magana da ƙarfi, kada kuwa ki ji tsoro. Ki faɗa wa garuruwan Yahuza, Cewa Allahnsu yana zuwa!


Ubangiji yana sanarwa ga dukan duniya, Cewa, “Ku ce wa jama'ar Urushalima, Ubangiji Mai Cetonku yana zuwa, Yana kawo mutanen da ya cece su.”


Ni kuma, Ubangiji, zan zama Allahnsu. Bawana Dawuda kuwa zai zama sarkinsu.’ Ni Ubangiji na faɗa.


Bawana Dawuda zai sarauce su. Dukansu za su sami shugaba guda. Za su bi ka'idodina su kiyaye dokokina.


Amma zan yi wa mutanen Yahuza jinƙai. Ni kaina zan cece su ba da baka ba, ba kuwa da takobi, ko da yaƙi, ka da dawakai, ko da sojojin dawakai ba.”


“Baitalami cikin Efrata, Wadda kike 'yar ƙarama a cikin kabilar Yahuza, Amma daga cikinki wani zai fito wanda zai sarauci Isra'ila Wanda asalinsa tun fil azal ne.”


Yakubu zai yi mulki, Zai hallaka waɗanda suka ragu cikin birni.”


Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali'u ne, marar girmankai, za ku kuwa sami kwanciyar rai.


“Ina wanda aka haifa Sarkin Yahudawa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, mun kuma zo mu yi masa sujada.”


“ ‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza, Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba, Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki, Wanda zai zama makiyayin jama'ata, Isra'ila.’ ”


Sai almajiran suka tafi suka bi umarnin Yesu.


Sai ya fara ta kan littattafan Musa da na dukan annabawa, ya yi ta bayyana musu abubuwan da suka shafe shi a dukan Littattafai.


Sai Nata'ala ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, kai Ɗan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!”


Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali'u da sanyin hali na Almasihu, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” ne a cikinku, amma “mai matsawa” ne sa'ad da nake rabe da ku,


Amma kada sarkin ya tattara wa kansa dawakai, kada kuma ya sa mutane su tafi Masar don su ƙaro masa dawakai, tun da yake Ubangiji ya riga ya yi muku kashedi da cewar, ‘Kada ku sāke komawa can.’


Yana da 'ya'ya maza arba'in, da jikoki maza talatin, suna hawan jakai saba'in. Abdon ya shugabanci Isra'ilawa shekara takwas.


Ku ba da labari, Ku da kuke haye da fararen jakuna, Kuna zaune a shimfiɗu, Ku da dole ku tafi da ƙafa duk inda za ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan