Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:43 - Littafi Mai Tsarki

43 “Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

43 “Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:43
13 Iomraidhean Croise  

za ku zama daular firistoci da al'umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne zantuttukan da za ka faɗa wa Isra'ilawa.”


A buɗe ƙofofin birnin, A bar amintacciyar al'umma ta shiga, Al'ummar da jama'arta take aikata abin da yake daidai.


Ubangiji yana da wani ƙaƙƙarfa mai iko a shirye don ya fāɗa musu da yaƙi. Zai zo kamar hadirin ƙanƙara, kamar kwararowar ruwan sama, kamar kuma rigyawa mai kirmewa wadda ta shafe ƙasa.


Ni kuwa in da ikon Ruhun Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan.


Sai suka ce masa, “Zai yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba waɗansu manoma sufurinta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”


Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini. Wannan aikin Ubangiji ne, A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’


Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje. Amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”


Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.”


Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba.


Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asiri, da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya, har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne.


Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan