4 An yi wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Zakariya cewa,
4 Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa,
Ki yi murna ƙwarai, ya Sihiyona! Ta da murya ya Urushalima! Ga Sarkinki yana zuwa wurinki, Shi mai adalci ne, mai nasara, Shi kuma mai tawali'u ne, Yana bisa kan jaki, a kan aholaki.
An yi wannan ne duk, don a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa,
Kowa ya yi muku magana, ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsu,’ zai kuwa aiko da su nan da nan.”
Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.
Suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfiɗa mayafansu a kai, ya hau.
Sai suka kawo shi wurin Yesu. Da suka shimfiɗa mayafansu a kan aholakin, suka ɗora Yesu.
Kashegari babban taron da suka zo idi, da suka ji Yesu yana zuwa Urushalima,
“Kada ki ji tsoro, ya ke 'yar Sihiyona, Ga sarkinki na zuwa a kan aholakin jaki!”