Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:38 - Littafi Mai Tsarki

38 Amma da manoman suka ga ɗan, suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin, ku zo mu kashe shi, gādonsa ya zama namu.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

38 “Amma da ’yan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:38
16 Iomraidhean Croise  

Yanzu kuwa dukan dangi sun tasar mini, suna cewa, in ba da ɗayan wanda ya kashe ɗan'uwansa domin su kashe shi saboda ran ɗan'uwansa da ya kashe. Wato za su hallaka magāji ke nan, ta haka za a yi biyu babu ke nan, su bar mijina ba suna ko zuriya a duniya.”


Yanzu sai ki zo in ba ki shawara domin ki tsira da ranki da na ɗanki Sulemanu.


Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar.


Daga baya sai ya aiki ɗansa gare su, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’


Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi.


Amma da manoman suka gan shi, suka yi shawara da juna suka ce, ‘Ai, wannan shi ne magajin. Mu kashe shi mana, gādon ya zama namu.’


amma a zamanin nan na ƙarshe, sai ya yi mana magana ta wurin Ɗansa, wanda ya sa magājin kome, wanda ta wurinsa ne kuma ya halicci duniya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan