Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:35 - Littafi Mai Tsarki

35 Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

35 “Amma ’yan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:35
23 Iomraidhean Croise  

Ashe, ba ka ji ba? Na kasa annabawan Ubangiji biyu, na ɓoye su a kogo hamsin hamsin, sa'ad da Yezebel ta kashe annabawan Ubangiji, na ciyar da su, na kuma shayar da su.


A lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji, Obadiya ya kwashe annabawa ɗari ya raba su hamsin hamsin ya ɓoye su a kogo, ya ciyar da su, ya shayar da su.


Ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, Allah Mai Runduna, kai kaɗai nake bauta wa kullayaumin. Amma jama'ar Isra'ila sun karya alkawarinka, sun rurrushe bagadanka, sun karkashe annabawanka, ni ne kaɗai na ragu, ga shi kuma, suna nema su kashe ni.”


Sai Yezebel ta aike a wurin Iliya ta ce, “Idan gobe war haka, ban kashe ka ba kamar yadda ka karkashe annabawan nan, to, alloli su hukunta ni.”


Sa'an nan Zadakiya ɗan Kena'ana ya matso kusa ya mari Mikaiya a fuska, ya ce, “Ƙaƙa Ruhun Ubangiji ya bar ni, ya zo ya yi magana da kai?”


Sai Asa ya yi fushi da maiganin, ya sa shi a kurkuku saboda maganar da ya yi masa, gama ya husata da shi ƙwarai. A wannan lokaci kuma sai Asa ya ƙuntata wa waɗansu daga cikin jama'a.


“Amma suka yi maka rashin biyayya, suka tayar maka, Suka juya wa dokokinka baya, Suka karkashe anna bawan da suka faɗakar da su, Waɗanda suka faɗa musu su juyo gare ka. Suka yi ta saɓa maka lokaci lokaci.


Na hori 'ya'yanku, amma a banza, ba su horu ba, Kun kashe annabawanku da takobi kamar mayunwacin zaki.


Sa'ad da Irmiya ya gama faɗar dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa wa dukan jama'a, sai firistoci, da annabawa, da dukan jama'a suka kama shi, suna cewa, “Mutuwa za ka yi!


Shugabanni suka yi fushi da Irmiya, suka yi masa dūka, suka tsare shi a gidan Jonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku.


Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar.


Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka.


Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a Sama, gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku.”


A cikin annabawa wane ne kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda a yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa,


Da ya ɓamɓare hatimi na biyar, na ga rayukan waɗanda aka kashe saboda Maganar Allah, da shaidar da suka yi a ƙarƙashin bagadin ƙona turare.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan