Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:31 - Littafi Mai Tsarki

31 To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da ubansu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 “Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?” Suka amsa, “Na farin.” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:31
26 Iomraidhean Croise  

Ba na bukata in kā da kai, Kowace kalma da ka hurta ta kā da ka.


Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?’


Ai, kowa ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so, shi ne ɗan'uwana, shi ne 'yar'uwata, shi ne kuma tsohuwata.”


ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in ba kun juyo kun zama kamar ƙananan yara ba, har abada ba za ku shiga Mulkin Sama ba.


Saboda haka na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma za su koma na ƙarshe.”


Sai ya je gun na biyun ya faɗa masa haka. Shi kuwa ya amsa ya ce, ‘To, za ni, baba,’ amma bai je ba.


Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome.


In masoyanku kawai kuke ƙauna, wane lada ne da ku? Ashe, ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba?


“In za ku yi addu'a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'u da kan hanya, wai mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun sami iyakar ladansu.


“Ba duk mai ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji,’ ne zai shiga Mulkin Sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so.


Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.


Haka nake gaya muku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah in mai zunubi guda ya tuba.”


Sai ya ce masa ‘Kai mugun bawa! Zan yi maka shari'a bisa ga abin da ka faɗa da bakinka. Ashe, ka sani ni mutum ne mai tsanani, mai son banza, ina kuma girbar abin da ba ni na shuka ba?


Da duk jama'a da masu karɓar haraji suka ji haka, suka tabbata Allah mai adalci ne, aka yi musu baftisma da baftismar Yahaya.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.”


Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba.


Dā kam, Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu yana umartar dukkan mutane a ko'ina su tuba,


To, mun sani duk abin da Shari'a ta ce, ya shafi waɗanda suke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma tă sani ƙarƙashin hukuncin Allah take.


Shari'a fa, an shigo da ita ne, don laifi yă haɓaka. Amma a inda zunubi ya haɓaka, alherin Allah ma ya fi haɓaka ƙwarai da gaske.


Ubangiji ba ya jinkirta alkawarinsa, yadda waɗansu suka ɗauki ma'anar jinkiri, amma mai haƙuri ne a gare ku, ba ya so kowa ya hallaka, sai dai kowa ya kai ga tuba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan