Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:28 - Littafi Mai Tsarki

28 “To, me kuka gani? An yi wani mutun mai 'ya'ya biyu maza. Ya je wurin na farkon, ya ce, ‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 “Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:28
13 Iomraidhean Croise  

Amma ya ce masa, “Ba zan tafi ba, zan koma ƙasata da wurin dangina.”


Ya ce, “I, yakan bayar.” Da ya dawo gida kuma, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce, “Me ka gani, Bitrus? Wurin wa sarakunan duniya suke karɓar kuɗin fito ko haraji, a wurin 'ya'yansu, ko kuwa daga wurin waɗansu?”


“Mulkin Sama kamar wani maigida yake, wanda ya fita da sassafe ya ɗauki ma'aikata don aikin garkarsa ta inabi.


Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”


Sai ya ce, ‘Na ƙi.’ Amma daga baya sai ya tuba, ya tafi.


“To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.


To, faɗa mana abin da ka gani. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?”


Kamar mutum ne mai tafiya, in ya bar gida ya wakilta yaransa, kowanne da aikinsa, ya kuma umarci mai jiran ƙofa ya zauna a faɗake.


Ko kuwa goma sha takwas ɗin nan da hasumiya ta faɗo a kansu, a Siluwam, ta kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?


Ina magana da ku a kan ku mahankalta ne fa, ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa.


Don haka, ya 'yan'uwana, ƙaunatattu, ku tsaya a kafe, kullum kuna himmantuwa ga aikin Ubangiji, domin kuwa kun san famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan