Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:26 - Littafi Mai Tsarki

26 In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ ai, muna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya ɗauki Yahaya a kan annabi ne.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 In kuma muka ce, ‘Daga mutane,’ muna tsoron mutane, gama duk sun ɗauka Yohanna annabi ne.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:26
17 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya ce, “Wa ya sa ku fargaba, kuke jin tsoronsa, har kuka yi ƙarya? Ba ku tuna da ni, ko ku kula da ni ba? Ashe, ban yi haƙuri tun da daɗewan nan ba, duk da haka kuwa ba ku ji tsorona ba?


To, don me kuka fita? Ku ga wani annabi? I, lalle kuwa, har ya fi annabi nesa.


Ko da yake yana son kashe shi, yana jin tsoron jama'a, don sun ɗauka shi annabi ne.


Sai jama'a suka ce, “Ai, wannan shi ne Annabi Yesu daga Nazarat ta ƙasar Galili.”


To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’


Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”


Amma da suka nemi kama shi, suka ji tsoron jama'a, don su sun ɗauke shi shi annabi ne.


Ma kuwa ce, ‘Ta mutum ce’?” Suna kuwa jin tsoron jama'a, don duk kowa ya tabbata, cewa Yahaya annabi ne.


Sai suka nemi su kama shi, don sun lura a kansu ne ya yi misalin, amma suna jin tsoron jama'a. Don haka suka ƙyale shi, suka tafi.


don Hirudus yana tsoron Yahaya, ya sani shi mutum ne adali, tsattsarka, shi ya sa ya kāre shi. Hirudus yakan damu da yawa sa'ad da yake sauraron Yahaya, ko da yake na murna da jinsa.


Nan take malaman Attaura da manyan firistoci suka nema su kama Yesu, don sun lura a kansu ne ya ba da misalin, amma suna jin tsoron jama'a.


In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ sai duk jama'a su jajjefe mu, don sun tabbata Yahaya annabi ne.”


Sai manyan firistoci da malaman Attaura suka yi ta neman yadda za su kashe shi, amma kuwa suna tsoron jama'a.


Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan.


Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla, cewa kowa ya amsa, cewa shi ne Almasihu, za a fisshe shi daga jama'a.


Sai shugaban dogaran Haikali da dogaran suka je suka kawo manzannin, amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada jama'a su jejjefe su da duwatsu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan