Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Sai Yesu ya shiga filin haikali, yayinda yake koyarwa, sai manyan firistoci da dattawan mutane suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka wannan iko?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:23
12 Iomraidhean Croise  

Ya amsa, ya ce, “Wa ya naɗa ka sarki ko alƙali a bisanmu? So kake ka kashe ni kamar yadda ka kashe Bamasaren?” Sai Musa ya tsorata, ya ce, “Assha, ashe, an san al'amarin!”


Sai ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi garkata, zan kuwa biya ku abin da yake daidai.’ Sai suka tafi.


Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. In kun ba ni amsa, ni ma sai in gaya muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan.


Yesu ya fita Haikalin, yana cikin tafiya, sai almajiransa suka zo suka nuna masa gine-ginen Haikalin.


Nan take Yesu ya ce wa taron jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? Kowace rana nakan zauna a Haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba.


Kowace rana ya yi ta koyarwa a Haikali. Amma manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka nema su hallaka shi.


Wata rana yana koyar da mutane a Haikali, yana yi musu bishara, sai ga manyan firistoci da malaman Attaura, da shugabanni suka matso,


Da suka tsai da su a tsakiya, suka tuhume su, suka ce, “Da wane iko ne, ko kuwa da wane suna ne, kuka yi haka?”


Amma mai cutar ɗan'uwa nasa ya ture Musa, ya ce, ‘Wa ya sa ka shugaba da alƙali a kanmu?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan