Har wa yau dai ina gaya muku, in mutum biyu daga cikinku, ra'ayinsu ya zo ɗaya a nan duniya a kan wani abin da za su roƙa, Ubana kuwa da yake Sama zai yi musu shi.
To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?
Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.