Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in dai kuna da bangaskiya, ba tare da wata shakka ba, ba abin da aka yi wa ɓauren nan kaɗai za ku yi ba, har ma in kun ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku,’ sai kuwa ya auku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:21
9 Iomraidhean Croise  

Ya ce, “Zo mana.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin, ya taka ruwa ya nufi gun Yesu.


Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Domin hakika ina gaya muku, da kuna da bangaskiya, ko misalin ƙwayar mustad, da za ku ce wa dutsen nan, ‘Kawu daga nan, ka koma can!’, sai kuwa ya kawu. Ba kuwa abin da zai gagare ku.


Da almajiran suka ga haka, suka yi mamaki suka ce, “Yaya ɓauren nan ya bushe haka nan da nan?”


'ya'yan Mulki kuwa sai a jefa su matsanancin duhu. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.”


Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asiri, da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya, har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne.


Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska take korawa tana tuttunkuɗawa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan