Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Da ya ga wani ɓaure a gefen hanya, ya je wurin, amma bai sami kome ba, sai ganye kawai. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada ka ƙara yin 'ya'ya har abada!” Nan take ɓauren ya bushe.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin ’ya’ya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:19
17 Iomraidhean Croise  

Ya kauce ƙasar ya tsintsince duwatsun, Ya daddasa itatuwan inabi mafi kyau. Ya gina hasumiya don a yi tsaronsu, Ya kuma haƙa rami inda za a matse 'ya'yan inabin. Ya yi ta jira don 'ya'yan inabin su nuna, Amma ko wannensu tsami take gare shi.


“Ni Ubangiji na ce, ‘Sa'ad da zan tattara su kamar amfanin gona, Sai na tarar ba 'ya'ya a kurangar inabi, Ba 'ya'ya kuma a itacen ɓaure, Har ganyayen ma sun bushe. Abin da na ba su kuma ya kuɓuce musu. Ni Ubangiji na faɗa.’ ”


Da almajiran suka ga haka, suka yi mamaki suka ce, “Yaya ɓauren nan ya bushe haka nan da nan?”


Sai ya ce wa ɓauren, “Kada kowa ya ƙara cin 'ya'yanka har abada!” Almajiransa kuwa suna ji.


Suna wucewa da safe, sai suka ga ɓauren nan ya bushe har saiwarsa.


Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin itatuwa. Saboda haka duk itacen da bai yi 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare shi, a jefa a wuta.”


Kowane reshe a cikina da ba ya 'ya'ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin 'ya'ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa.


Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone.


suna riƙe da siffofin ibada, amma suna sāɓa wa ikonta. Ka yi nesa da irin waɗannan mutane.


Suna cewa sun san Allah, amma suna sāɓa masa ta wurin aikinsu. Abin ƙyama ne su, kangararru, ko kaɗan ba su da wani amfani a wajen yin aiki nagari.


Waɗannan mutane kamar aibobi ne a taronku na soyayya, suna ta shagulgulan ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro, suna kula da kansu kawai. Su kamar holoƙon hadiri ne, wanda iska take korawa. Su kamar itatuwa ne, marasa 'ya'ya da kaka, matattu murus, tumɓukakku.


Marar gaskiya yă yi ta rashin gaskiyarsa, fajiri kuwa yă yi ta fajircinsa, adali kuwa yă yi ta aikata adalcinsa, wanda yake tsattsarka kuwa ya yi ta zamansa na tsarki.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan