18 Kashegari da sassafe yana komowa birni, sai ya ji yunwa.
18 Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa.
A lokacin nan a ran Asabar, Yesu yana ratsa gonakin alkama. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara zagar alkamar suna ci.
Da ya yi azumi kwana arba'in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi.
har kwana arba'in, Iblis yana gwada shi. A kwanakin nan bai ci kome ba. Da suka ƙare kuwa ya ji yunwa.
Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a'a, shi ne wanda aka jarabce shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba.