Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Sai Yesu ya shiga Haikalin ya kakkori dukkan masu saye da sayarwa a ciki, ya birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:12
18 Iomraidhean Croise  

Dukan wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar kuwa zai biya kuɗi bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Tilas kowanne ya biya wannan, gama sadaka ce ga Ubangiji.


Idan kuma hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji daga cikin tsuntsaye ne, sai ya kawo kurciyoyi, ko 'yan tattabarai.


Sa'ad da kwanakin tsarkakewarta na haihuwar ɗa ko 'ya suka cika, sai ta kai wa firist ɗan rago bana ɗaya, a ƙofar alfarwa ta sujada don hadaya ta ƙonawa, da ɗan tattabara, ko kurciya na yin hadaya don zunubi.


Amma idan ɗan rago ya fi ƙarfinta, sai ta kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu, ɗaya don hadaya ta ƙonawa, ɗayan kuwa don yin hadaya don zunubi. Firist kuwa zai yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka.


da kuma kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu yadda dai ya iya. Ɗayan domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa.


Sai mutumin ya ba da kurciyoyi, ko 'yan tattabarai yadda ya iya,


A kan rana ta takwas zai kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada, ya ba firist.


A rana ta takwas sai ta kawo 'yan kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai, a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada.


Amma idan har kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu sun fi ƙarfinsa don yin hadaya saboda laifinsa, sai ya kawo humushin garwar gari mai laushi don yin hadaya saboda laifinsa. Ba zai zuba mai ko lubban a garin ba, gama hadaya ce don laifi.


Amma idan 'yar tunkiyar ta fi ƙarfinsa, sai ya kawo kurciyoyi biyu ko 'yan tattabarai biyu don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifin da ya yi. Ɗaya za ta zama ta yin hadaya don laifi, ɗayan kuwa don yin hadaya ta ƙonawa.


Sai ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Da dai ya dudduba kome, da yake magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyun nan.


su kuma yi hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Shari'ar Ubangiji cewa, “Kurciyoyi biyu, ko kuwa 'yan shila biyu.”


Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan