Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Da ya shiga Urushalima dukkan birnin ya ruɗe, ana ta cewa, “Wane ne wannan?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:10
14 Iomraidhean Croise  

Wane ne wannan da yake fitowa daga cikin jeji, Kamar tunnuƙewar hayaƙi cike da kayan ƙanshi iri iri na fatake?


Wane ne wannan da yake zuwa daga Bozara cikin Edom? Wane ne wannan da ya sha ado da jajayen kaya, yana tafe, ga shi kuwa ƙaƙƙarfa? Ubangiji ne, mai ikon yin ceto, yana zuwa ya yi sanarwar nasara.


Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu ƙwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima.


Sai jama'a suka ce, “Ai, wannan shi ne Annabi Yesu daga Nazarat ta ƙasar Galili.”


Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!”


suka ce masa, “Gaya mana da wane izini kake yin abubuwan nan, ko kuwa wa ya ba ka izinin?”


Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara wuswasi cewa, “Wane ne wannan da yake maganar saɓo? Wa yake iya gafarta zunubi banda Allah shi kaɗai?”


Masu ci tare da shi kuwa suka fara ce wa juna, “Wannan kuwa wane ne wanda har yake gafarta zunubai?”


Sai Hirudus ya ce, “Yahaya kam na fille masa kai. Wa ke nan kuma da nake jin irin waɗannan abubuwa game da shi?” Sai ya nemi ganinsa.


Sai Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Wace mu'ujiza za ka nuna mana da kake haka?”


Shi kuma ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Sai ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.


Su biyu kuwa suka kama hanya har suka isa Baitalami. Da suka isa Baitalami, sai dukan garin ya ruɗe saboda su. Mata suka ce, “Na'omi ce wannan?”


Sama'ila ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa, ya tafi Baitalami, inda dattawan garin suka tarye shi da rawar jiki, suka ce masa, “Maigani, wannan ziyara lafiya kuwa?”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan