Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 20:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Sai suka ce masa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi garkata.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 “Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ “Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 20:7
16 Iomraidhean Croise  

Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka, domin ba aiki, ko tunani, ko ilimi, ko hikima a lahira, gama can za ka.


“Mulkin Sama kamar wani maigida yake, wanda ya fita da sassafe ya ɗauki ma'aikata don aikin garkarsa ta inabi.


Wajen la'asar kuma ya fita ya sami waɗansu a tsaitsaye, ya ce musu, ‘Don me kuke zaman banza yini zubur?’


Da magariba ta yi, mai garkar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kirawo ma'aikatan, ka biya su hakkinsu, ka fara daga na ƙarshe har zuwa na farko.’


Lalle ne mu yi aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai, dare zai yi sa'ad da ba mai iya aiki.


suka ce, “Yaya za mu yi da mutanen nan? Don hakika sanannen abu ne ga dukan mazauna Urushalima, cewa an yi wata tabbatacciyar mu'ujiza ta wurinsu, ba mu kuwa da halin yin mūsawa.


Ɗaukaka tă tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa'azin Yesu Almasihu, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil'azal.


Kun sani, kowane alherin da mutum ya yi, ko shi ɗa ne ko bawa, Ubangiji zai sāka masa shi.


wato, asirin nan da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, amma a yanzu an bayyana shi ga tsarkakansa.


Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan