Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 20:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Domin tausayi, sai Yesu ya taɓa idanunsu, nan take suka gani, suka bi shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 20:34
20 Iomraidhean Croise  

Kafin ka hore ni nakan yi kuskure, Amma yanzu ina biyayya da maganarka.


Horon da aka yi mini ya yi kyau, Domin ya sa na koyi umarnanka.


Ubangiji mai ƙauna ne, mai jinƙai, mai jinkirin fushi, Cike da madawwamiyar ƙauna.


Da ya fita daga jirgin ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu.


Yesu ya kira almajiransa, ya ce, “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna ba su da wani abinci. Ba na kuwa so in sallame su da yunwa haka, kada su kasa a hanya.”


Suka ce masa, “Ya Ubangiji, mu dai mu sami gani!”


Da suka kusato Urushalima suka zo Betafaji, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu,


Sai ya taɓa hannunta, zazzaɓin ya sake ta, ta kuma tashi ta yi masa hidima.


Sa'an nan ya taɓa idanunsu, ya ce, “Yă zama muku gwargwadon bangaskiyarku.”


Amma da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, domin suna shan wahala, suna nan a warwatse kamar tumaki da ba makiyayi.


Yesu ya ɗauke shi suka koma waje ɗaya, rabe da taron, ya sa yatsotsinsa a kunnuwansa, ya tofar da yau, ya kuma taɓa harshensa.


Nan take ya sami gani, ya bi Yesu, yana ɗaukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.


Yesu ya amsa ya ce, “Ku ƙyale su haka.” Sai ya taɓa kunnen bawan, ya warkar da shi.


Da Ubangiji ya gan ta, ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, “Daina kuka.”


domin ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan tsarkaka saboda sun gaskata da ni.’ ”


Saboda haka, lalle ne yă zama kamar 'yan'uwansa ta kowane hali, domin yă zama Babban Firist, mai jinƙai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a.


Daga ƙarshe kuma dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar 'yan'uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali'u.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan