Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 20:30 - Littafi Mai Tsarki

30 Ga mutum biyu makafi zaune a bakin hanya. Da suka ji dai Yesu ne yake wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Ubangiji, ka ji tausayinmu, ya Ɗan Dawuda!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 20:30
21 Iomraidhean Croise  

Yakan ba makafi ganin gari. Yakan ɗaukaka waɗanda aka wulakanta. Yana ƙaunar jama'arsa, adalai.


A wannan rana, kurame za su ji sa'ad da aka karanta littafi da murya, makafi kuwa waɗanda suke zaune cikin duhu za su buɗe idanunsu su gani.


“Zan yi wa mutanena makafi jagora A hanyar da ba su taɓa bi ba. Zan sa duhunsu ya zama haske, In kuma sa ƙasa mai kururrumai ta zama sumul a gabansu. Ba zan kasa yin waɗannan abu ba.


Ubangiji ya ce, “Ku kasa kunne, ya ku kurame! Ku duba da kyau sosai, ku makafi!


Muna ta lalubar bango kamar makafi, muna ta lalubawa kamar marasa idanu. Da tsakar rana muke ta tuntuɓe, sai ka ce da almuru. A tsakanin waɗanda suke da cikakken ƙarfi, kamar matattu muke.


Yana cikin yafa iri sai waɗansu ƙwayoyi suka faɗa a hanya, sai tsuntsaye suka zo suka tsince su.


Ga wata Bakan'aniya mutuniyar ƙasar, ta zo, ta ɗaga murya ta ce, “Ya Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina. Wani aljani ya bugi 'yata, ba yadda take.”


Jama'a suka kwaɓe su su yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya suke yi ƙwarai da gaske, suna cewa, “Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, ya Ɗan Dawuda!”


Sai makafi da guragu suka zo wurinsa a Haikalin, ya kuwa warkar da su.


Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!”


ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wane ne?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.”


Sai suka iso Yariko. Yana fita daga Yariko ke nan, da shi, da almajiransa, da wani ƙasaitaccen taro, sai ga wani makaho mai bara, wai shi Bartimawas, ɗan Timawas, yana zaune a gefen hanya.


“Ruhun Ubangiji yana tare da ni, Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara. Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru, In kuma buɗe wa makafi ido, In kuma 'yanta waɗanda suke a danne,


Nan take Yesu ya warkar da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cuce-cucensu da kuma baƙaƙen aljannu. Makafi da yawa kuma ya yi musu baiwar gani.


To, da yake shi annabi ne, ya kuma san Allah ya rantse masa, cewa zai ɗora wani daga cikin zuriya tasa kan kursiyinsa,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan