Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 20:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Wajen ƙarfe tara kuma da ya fita, sai ya ga waɗansu suna zaman banza a bakin kasuwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 “Wajen sa’a ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 20:3
12 Iomraidhean Croise  

Rago, yi ta ragwancinka ka yi ta sharar barci, amma kai za ka sha yunwa.


Wannan shi ne laifin Saduma, ƙanwarki, ita da 'ya'yanta mata, suna da girmankai domin suna da abinci a wadace, suna zama a sangarce, amma ba su taimaki matalauta da masu bukata ba.


Da ya yi lada da su a kan dinari guda a yini, sai ya tura su garkarsa.


Sai ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi garkata, zan kuwa biya ku abin da yake daidai.’ Sai suka tafi.


Da ƙarfe tara na safe suka gicciye shi.


Da iyayengijinta suka ga hanyar samunsu ta toshe, suka danƙe Bulus da Sila, suka ja su har zuwa bakin kasuwa gaban mahukunta.


Ai, mutanen nan ba bugaggu ba ne yadda kuke zato, tun da yake yanzu ƙarfe tare na safe ne kawai.


Banda haka kuma sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida gida. Ba ma kawai masu zaman banza za su zama ba, har ma sai su zama matsegunta, masu shishigi, suna faɗar abin da bai kamata ba.


don kada ku yi ragwanci, sai dai ku yi koyi da waɗanda suka karɓi cikar alkawaran nan, ta wurin bangaskiyarsu da haƙurinsu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan