27 Wanda duk kuma yake so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawanku,
27 kuma duk mai son zama shugaba, dole yă zama bawanku,
Duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar ɗan yaron nan, ai, shi ne mafi girma a Mulkin Sama.
Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku.
kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba sai dai domin shi ya yi bautar, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
Amma ku kam ba haka ba. Sai dai wanda yake babba a cikinku yă zama kamar ƙarami, shugaba kuwa yă zama kamar mai hidima.
Akwai hakkin Helenawa, da na bare, da na masu ilimi, da na jahilai duka a kaina.
A ganina ban kasa mafifitan manzannin nan da kome ba.
Ni kam, zan kashe dukan abin hannuna da dukan zarafina da matuƙar farin ciki saboda ranku. In na ƙara ƙaunarku, ashe, sai a rage ƙaunata?
Domin ba wa'azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Almasihu a kan shi ne Ubangiji, mu kuwa bayinku ne saboda Yesu.