Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 20:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Ba haka zai kasance da ku ba. Maimakon haka, duk mai son zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 20:26
23 Iomraidhean Croise  

Ya Urushalima, tsatsarki ita ce ƙazantar lalatarki. Da yake na tsabtace ki, ba ki tsabtatu ba, To, ba za ki ƙara yin tsabta ba, Har lokacin da na fashe fushina a kanki.’


Wanda duk kuma yake so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawanku,


Sa'an nan su ma za su amsa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa, ko da ƙishirwa, ko da baƙunci, ko da huntanci, ko da rashin lafiya, ko a kurkuku, ba mu kula da kai ba?’


Akwai kuma waɗansu mata da yawa a can suna hange daga nesa, waɗanda suka biyo Yesu tun daga ƙasar Galili, suna yi masa hidima.


Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku.


Domin Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi ya yi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”


Sai ya zauna, ya kira sha biyun nan, ya ce musu, “Kowa yake son yă zama shugaba, lalle ne yă zama na ƙarshe duka, baran kowa kuma.”


Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”


Amma ku kam ba haka ba. Sai dai wanda yake babba a cikinku yă zama kamar ƙarami, shugaba kuwa yă zama kamar mai hidima.


Yesu ya amsa ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaƙi kada a bāshe ni ga Yahudawa. Amma hakika, mulkina ba daga nan yake ba.”


Da suka kai Salamis, suka sanar da Maganar Allah a majami'un Yahudawa, ga kuma Yahaya na taimakonsu.


Ba cewa muna nuna muku iko a kan bangaskiyarku ba ne, a'a, sai dai muna aiki tare ne, domin ku yi farin ciki, domin a game da bangaskiyarmu kam, kuna tsaye kankan.


Ubangiji ya yi masa jinƙai a waccan rana. Ka dai sani sarai yadda ya yi ɗawainiya mai yawa a Afisa.


Dā kam sona in riƙe shi a wurina, yă riƙa yi mini hidima a madadinka, muddin ina ɗaure saboda bishara.


Ashe, dukan mala'iku ba ruhohi masu hidima ba ne, waɗanda Allah yakan aika, don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?


Duk mai wa'azi yă dai san faɗar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, domin a cikin al'amura duka a ɗaukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!


Kada ku nuna wa waɗanda suke hannunku iko, sai dai ku zama abin koyi ga garken nan.


Sai na ga matar ta bugu da jinin tsarkaka, da kuma jinin mashaidan Yesu. Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai da gaske.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan