Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 20:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya shan ƙoƙon da ni zan sha?” Suka ce masa, “Ma iya.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?” Suka amsa, “Za mu iya.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 20:22
17 Iomraidhean Croise  

Ko da duniya da dukan waɗanda yake zaune cikinta za su ɓace, Zan ƙarfafa harsashin gininta.


Girmankai jagora ne zuwa ga hallaka, fāriya kuwa zuwa ga fāɗuwa.


Ya Urushalima, ki farka! Ki tashi da kanki, ki miƙe! Kika sha ƙoƙon hukunci wanda Ubangiji, cikin fushinsa, ya ba ki ki sha, Kika shanye shi, ya kuwa sa ki yi tangaɗi!


Ubangiji Allahnku ya kāre ku ya ce, “Ina ɗauke ƙoƙon da na ba ku cikin fushina. Ba za ku ƙara shan ruwan inabin da zai sa ku yi tangaɗi ba.


Ubangiji ya ce, “Ga shi, waɗanda ba a shara'anta su ga shan ƙoƙon hukunci ba, za su sha shi, to, kai za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, amma lalle za ka sha shi!


Bitrus ya ce masa, “Ko za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Haka ma duk almajiran suka ce.


Da ya ci gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubana, in mai yiwuwa ne, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalar nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.”


Har wa yau a komawa ta biyu, sai ya je ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubana, in wannan ba zai wuce ba sai na sha shi, to, a aikata nufinka.”


Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.


Sa'an nan ya ce, “Ya Abba, Uba, kowane abu mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.”


Ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa ɗokanta ƙwarai har a yi mini ita!


Ya ce, “Ya Uba, in dai ka yarda, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai, ba nufina ba, sai naka za a bi”


Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Mai da takobinka kube. Ba sai in sha ƙoƙon da Uba ya ba ni in sha ba?”


Haka kuma Ruhu yake yi mana taimako a kan gajiyawarmu, domin ba mu ma san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu da kansa yana yi mana roƙo da nishe-nishen da ba su hurtuwa.


Kukan yi addu'a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku ɓatar a kan nishaɗinku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan