Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 20:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Sai ya ce mata, “Me kike bukata?” Ta ce masa, “Ka yi umarni waɗannan 'ya'yana biyu su zauna, ɗaya a damanka, ɗaya a hagunka, a mulkinka.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Ya yi tambaya ya ce, “Mene ne kike so?” Ta ce, “Ka sa daga cikin ’ya’yan nan nawa biyu, ɗaya yă zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 20:21
24 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan Bat-sheba ta tafi wurin sarki Sulemanu don ta yi magana da shi a kan Adonija. Sarki ya tashi domin ya tarye ta. Ya rusuna mata, sa'an nan ya zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo mata kujera, ta kuwa zauna a wajen damansa.


Ubangiji kuwa ya bayyana ga Sulemanu cikin mafarki a Gibeyon da dare, ya ce masa, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”


Sarki ya ce mata, “Mene ne, sarauniya Esta? Me kike so? Za a ba ki, ko rabin mulkina ma.”


Ubangiji ya ce wa Mai Girma, Sarkina, “Zauna nan a damana, Har in sa maƙiyanka a ƙarƙashin sawayenka.”


Daga cikin matan da suke fadarka, har da 'ya'yan sarakuna. A daman kursiyinka kuwa ga sarauniya a tsaye. Tana saye da kayan ado na zinariya mafi kyau duka.


Kana nemar wa kanka manyan abubuwa? Kada ka neme su, gama zan kawo masifa a kan dukan 'yan adam, amma zan kuɓutar da ranka kamar ganima, a dukan wuraren da za ka tafi.’ ”


A lokacin nan almajirai suka zo wurin Yesu, suka ce, “Wa ya fi girma duka a Mulkin Sama?”


Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, a sabon zamani, sa'ad da Ɗan Mutum ya zauna a maɗaukakin kursiyinsa, ku da kuka bi ni, ku ne kuma za ku zauna a kursiyi goma sha biyu, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila.


Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya shan ƙoƙon da ni zan sha?” Suka ce masa, “Ma iya.”


Sai Yesu ya tsaya, ya yi kiransu ya ce, “Me kuke so in yi muku?”


Yesu ya ce masa, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce masa, “Malam, in sami gani!”


To, bayan da Ubangiji Yesu ya yi musu jawabi, aka ɗauke shi aka kai shi Sama, ya zauna dama ga Allah.


Da 'yar Hirudiya ta shigo ta yi rawa, sai ta gamshi Hirudus da baƙinsa. Sai fa sarki ya ce wa yarinyar, “Roƙe ni kome, sai in ba ki.”


“Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ya Ubangiji, in sami gani!”


Da suka ji abubuwan nan, Yesu ya ci gaba da gaya musu wani misali, gama yana kusa da Urushalima, suna kuma tsammani Mulkin Allah zai bayyana nan da nan.


Sai musu ya tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne babbansu.


In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku.


Saboda haka da suka taru, suka tambaye shi suka ce, “Ya Ubangiji, yanzu ne za ka sāke kafa wa Isra'ila mulki?”


A game da ƙaunar 'yan'uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa yă riga ba ɗan'uwansa.


Wa zai hukunta su? Almasihu Yesu wanda ya mutu, ko kuwa a ce wanda ya tashi daga matattu, shi ne wanda yake zaune dama ga Allah, shi ne kuwa wanda yake roƙo saboda mu!


To, da yake an tashe ku tare da Almasihu, sai ku nemi abubuwan da suke a Sama, inda Almasihu yake, a zaune a dama ga Allah.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan